Shugaba Tinubu ya Sha Alwashin ceto Dalibai da Malaman da aka Sace a Jihar Oyo.

Shugaba Tinubu ya Sha Alwashin ceto Dalibai da Malaman da aka Sace a Jihar Oyo.

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta yi iya bakin kokarinta wajen ganin an kubutar da dalibai da malamansu da aka yi garkuwa da su a Jihar Oyo.

A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Tinubu ya bayyana cewa jami’an tsaro na ci gaba da amfani da sahihan bayanan sirri da dabarun aiki na musamman domin gano inda wadanda aka sace suke da kuma ceto su cikin koshin lafiya.

Ya ce an bai wa hukumomin tsaro cikakken umarni da kayan aikin da suke bukata domin gudanar da aikin ceto cikin gaggawa da nasara.

Shugaban kasar ya kuma nuna matukar alhininsa kan kisan wani malamin makaranta da aka yi yayin harin da masu garkuwa da mutane suka kai a karamar hukumar Oriire, inda suka yi awon gaba da dalibai da malamai.

Tinubu ya jaddada kudirin gwamnatinsa na tabbatar da tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Najeriya.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *