Dakarun Operation Hadin Kai Sun Ceto Mutane 92 Daga Hannun Boko Haram A Arewa Maso Gabas

Dakarun Operation Hadin Kai Sun Ceto Mutane 92 Daga Hannun Boko Haram A Arewa Maso Gabas

Dakarun tsaro na haɗin gwiwa ƙarƙashin rundunar Operation Hadin Kai sun kuɓutar da fararen hula 92 da mayaƙan Boko Haram da ISWAP suka yi garkuwa da su a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Mai magana da yawun rundunar, Laftanar Kanal Sani Uba, ya bayyana cewa an gudanar da aikin ceton ne bayan samun bayanan sirri kan yadda ‘yan ta’addan suka tare matafiya a hanyar Damaturu zuwa Biu tare da yin awon gaba da su.

A cewarsa, mutanen da aka ceto sun haɗa da maza 52, mata 33 da ƙananan yara bakwai, waɗanda aka kuɓutar daga wurare daban-daban a jihohin Borno, Adamawa da Yobe.

Sanarwar ta ce da misalin ƙarfe 11:00 na dare ne Bataliya ta 135 ta samu rahoton lamarin, inda nan take dakarun suka tunkari yankin Dutsen Kura da ake zargin ‘yan ta’addan suna tsare da mutanen da suka sace.

Ta ƙara da cewa mayaƙan Boko Haram da ISWAP sun yi yunƙurin hana dakarun isa wurin ta hanyar dasa abubuwan fashewa a kan hanyar Bula Zarma zuwa Mangari, amma dukkan na’urorin fashewar sun kasa aiki.

Rundunar ta kuma sanar da cewa an ƙwato motoci takwas a yayin aikin, tare da tabbatar da cewa babu wani jami’in tsaro da ya rasa ransa ko ya samu mummunan rauni a lokacin samamen.

Ta jaddada cewa dakarun Operation Hadin Kai za su ci gaba da kai hare-hare kan maboyar ‘yan ta’adda domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma a yankin Arewa maso Gabas.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *