An sanar da sakamakon zaɓen ne a Abuja a daren Laraba, inda jami’in gudanar da zaɓen, Tunde Ogbeha, ya bayyana cewa Atiku ya samu jimillar ƙuri’u 1,855,787.
Tsohon gwamnan Jihar Ribas, Rotimi Amaechi, ya zo matsayi na biyu bayan samun ƙuri’u 509,397, yayin da fitaccen ɗan kasuwa Mohammed Hayatu-Deen ya samu ƙuri’u 180,903.
Sai dai yayin tattara sakamakon zaɓen, Amaechi da Hayatu-Deen sun nuna rashin amincewa da tsarin zaɓen, suna masu zargin cewa an samu kura-kurai da matsaloli a yadda aka gudanar da shi.
Duk da haka, kakakin jam’iyyar ADC, Bolaji Abdullahi, ya ce an gudanar da zaɓen cikin gaskiya da adalci ba tare da wata matsala ba.
Atiku ya yi nasara a jihohi da dama da suka haɗa da Kano, Adamawa, Sakkwato, Kebbi, Gombe da Zamfara, inda ya samu rinjayen ƙuri’u sosai.
Amaechi kuwa ya samu nasara ne kawai a Jihar Akwa Ibom, inda ya kayar da Atiku da tazarar ƙuri’u kaɗan.
A wasu daga cikin sakamakon jihohi:
Kano: Atiku ya samu ƙuri’u 155,595, Amaechi kuma ya samu 9,994.
Adamawa: Atiku ya samu 177,141, yayin da Amaechi ya samu 1,896.
Gombe: Atiku ya samu 136,933, Amaechi kuma ya samu 1,140.
Akwa Ibom: Amaechi ya samu 20,343, Atiku ya samu 17,623.
Abuja: Atiku ya samu 18,704, Amaechi kuma ya samu 14,721.
Nasarar Atiku a wannan zaɓe na fid-da-gwani na ADC na ƙara nuna shirye-shiryen jam’iyyar na tunkarar babban zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa a Najeriya.
