Ana sa ran za a ga rana ta kasance a tsaye daidai  saman dakin Ka’aba a ranar Babbar Sallah 27 ga watan Mayu, 2026.

Ana sa ran za a ga rana ta kasance a tsaye daidai saman dakin Ka’aba a ranar Babbar Sallah 27 ga watan Mayu, 2026.

Da misalin karfe 12:18 na rana agogon Makkah, hasken rana zai ratsa daidai saman Ka’aba, wadda ke zama alkiblar Musulmi a duk duniya.

Masana sun bayyana cewa wannan yanayi na musamman yana bai wa Musulmi da ke kasashe daban-daban damar tantance sahihiyar alkiblar da suke fuskanta yayin gudanar da sallah, musamman idan suka yi amfani da inuwa ko alkibla a wannan lokaci.

Abin lura shi ne, wannan karo na farko cikin shekaru 139 da rana za ta kasance a irin wannan matsayi a ranar Babbar Sallah, ranar da alhazai ke gudanar da muhimman ibadoji kamar Jifan Shaidan, yanka hadaya, aski da kuma Dawafin Hajji.

A lokaci guda kuma, Musulmi mazauna gida a sassan duniya za su kasance suna gudanar da bukukuwan Eidil Kabir da ibadar Layya, wanda ya dace da ranar 10 ga watan Zul-Hijja.

Masana ilimin taurari sun ce wannan al’amari yana faruwa ne saboda yadda duniya ke juyawa tare da tafiyar rana tsakanin yankunan Tropic of Cancer da Tropic of Capricorn.

 

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *