Wani malamin makaranta ya shiga hannun ‘yan sanda bisa zargin kashe wata dalibar da ke shirin rubuta jarabawar WASSCE  mai shekaru 16.

Wani malamin makaranta ya shiga hannun ‘yan sanda bisa zargin kashe wata dalibar da ke shirin rubuta jarabawar WASSCE mai shekaru 16.

Rahotanni sun bayyana cewa ya yaudare ta zuwa wajen da aka kashe ta da sunan zuwa karatun koyarwa na musamman. Bayan haka, ana zarginsa da neman kudin fansa na Naira 500,000 daga mahaifin yarinyar, inda ya amsa cewa ya kashe kudin wajen caca ta yanar gizo.

 

Bincike ya nuna cewa bayan Florence ta bar makarantar da yake koyarwa, ya sake tuntubarta bayan kusan shekara guda sannan ya yi kokarin hada ta da wani abokinsa mai suna Sola domin soyayya. Ana zargin ya tsare ta a wani ginin da ba a kammala ba sannan ya bata maganin barci na D5 fiye da kima, wanda ya yi sanadin mutuwarta. Daga baya ya jefa gawarta cikin wani kogi a Ogijo bayan ya yi zaton ta mutu. Duk da cewa ya ce mutuwar kuskure ce, ‘yan sanda sun gano yana da hannu a damfarar intanet.

 

A cikin bayanin da ya yi wa ‘yan sanda, Baiyegun ya ce ya sake haduwa da Florence ne a watan Afrilu yayin da yake daukar bidiyo don shafinsa na Instagram. Ya bayyana cewa ya gayyace ta zuwa makarantar da yake koyarwa inda ya hada ta da abokinsa Sola. Bayan Sola ya nemi yin lalata da ita kuma ta ki amincewa, Florence ta nemi kudin mota daga gare shi amma ya ce ba shi da kudi. Daga baya, a cewarsa, sun shirya karya satar mutane domin karbar kudi daga iyalanta, amma lamarin ya rikide zuwa mutuwa.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *