Makinde ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi yayin da yake ganawa da manema labarai kan halin tsaro bayan wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun mamaye makarantun.
Gwamnan ya ce tun da farko ya gana da kwamandojin jami’an tsaro da shugabannin hukumomin tsaro na jihar domin samun bayanai kan lamarin.
A cewarsa, an kashe wani malamin addinin Musulunci a harin, yayin da jami’an tsaro suka kama mutane shida a cikin al’ummar yankin da kuma wasu mutum uku da ake zargi suna da hannu a lamarin.
Makinde ya tabbatar wa mazauna jihar cewa ana ci gaba da ƙoƙarin ceto waɗanda aka sace tare da ƙarfafa tsaro a makarantu da sauran al’ummomin da ke cikin haɗari a jihar.
