Rikicin tsaro da ke ƙara muni a Najeriya ya sake ɗaukar sabon salo bayan da rahotanni suka bayyana cewa ƴan ta’adda sun sace ɗalibai 42 a jihar Borno.

Rikicin tsaro da ke ƙara muni a Najeriya ya sake ɗaukar sabon salo bayan da rahotanni suka bayyana cewa ƴan ta’adda sun sace ɗalibai 42 a jihar Borno.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da rundunar sojin Najeriya tare da haɗin gwiwar sojojin Amurka suka sanar da kashe wani babban kwamandan ƙungiyar ISIS mai suna Abu-Bilal al-Minuki a wani samame da suka kai yankin Tafkin Chadi cikin dare. Haka kuma, an ce an gudanar da irin wannan farmaki kan ƴan ta’adda a Sokoto tare da haɗin gwiwar Amurka a watan Disambar shekarar 2025.

Sanata Ali Ndume ya tabbatar da cewa mayaƙan Boko Haram da ISWAP sun kai hari makarantar firamare da ƙaramar sakandare ta gwamnati da ke Mussa a ƙaramar hukumar Askira-Uba, inda suka yi awon gaba da yara da ɗalibai yayin da ake gudanar da karatu da safe ranar Juma’a. A cewarsa, an sace ɗalibai huɗu daga sashen sakandare, yara 28 daga firamare, sannan wasu yara 10 daga gidajensu, lamarin da ya kai jimillar mutanen da aka sace zuwa 42. Ya bayyana harin a matsayin abin takaici da tausayi wanda ya jefa iyalai cikin jimami.

Ndume ya yi kira ga jami’an tsaro da su ƙara ƙaimi wajen ceto waɗanda aka sace tare da dawo da zaman lafiya a yankin Borno. Ya kuma nuna damuwa kan yadda hare-haren ƴan ta’adda suka sake ƙaruwa a kudancin Borno, musamman a yankunan Chibok. Sabbin hare-haren sun sake tunatar da al’umma mummunan tarihin sace ‘yan mata na Chibok a shekarar 2014 da sauran hare-haren makarantu da suka addabi Arewa maso Gabashin Najeriya cikin shekaru da suka gabata.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *