Jigo a Jam’iyyar NDC, Injiniya Buba Galadima, ya bayyana cewa akwai yiwuwar a kayar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu cikin sauƙi a babban zaɓen Shekarar 2027.

Jigo a Jam’iyyar NDC, Injiniya Buba Galadima, ya bayyana cewa akwai yiwuwar a kayar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu cikin sauƙi a babban zaɓen Shekarar 2027.

Galadima ya bayyana hakan ne yayin wata hira da BBC Hausa, inda ya ce sakamakon zaɓen 2023 ya nuna cewa samun sauyin gwamnati abu ne mai yiwuwa idan aka tsara siyasa yadda ya kamata.

A cewarsa, Shugaba Tinubu ya samu kusan ƙuri’u miliyan takwas ne kacal a zaɓen da ya gabata, yana mai cewa irin waɗannan ƙuri’u za a iya tara su daga jihohi biyu kacal a yankin Arewa.

Ya ƙara da cewa idan al’ummar Kano da Katsina suka haɗa kai tare da mara wa ɗan takara guda baya, hakan kaɗai na iya sauya akalar zaɓen shugaban ƙasa.

Kalaman na Buba Galadima na zuwa ne yayin da jam’iyyun siyasa da manyan ’yan siyasa suka fara shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027, inda ake ci gaba da tattaunawa kan sabbin dabarun neman mulki ko kare kujerun da suke kai.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *