Kotun tace hakan ya faru ne bayan ya kasa bayyana a gaban kotu domin ci gaba da shari’ar da ake yi masa kan zargin almundahanar kuɗi har Naira biliyan 31.
Mai Shari’a Maryanne Anenih ce ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar Alhamis sakamakon rashin halartar da Mamman ya yi a zaman kotun na ranar Litinin.
Wannan mataki na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan wata kotu a Abuja ta bayar da irin wannan umarni, inda aka tuhume shi da karkatar da Naira biliyan 33.8 a wani shari’a daban da ke da alaƙa da ayyukan samar da wutar lantarki.
Hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon ministan tare da wasu mutum bakwai bisa zargin haɗa baki wajen karkatar da kuɗaɗen da aka ware domin ayyukan lantarki, ciki har da na tashoshin Zungeru da Mambilla.
A zaman kotun na baya-bayan nan, duk sauran waɗanda ake tuhuma sun halarta, sai dai Saleh Mamman kaɗai ne bai bayyana ba, lamarin da ya sa lauyan gwamnati, Rotimi Oyedepo, ya buƙaci kotu ta bayar da umarnin kamo shi tare da ci gaba da shari’ar.

