Sufeto Janar na ‘Yansandan Najeriya  Olatunji Disu ya bada umarnin bincike kan zargin jami’an ’yan sanda da hannu a ɓacewar Dadiyata.

Sufeto Janar na ‘Yansandan Najeriya Olatunji Disu ya bada umarnin bincike kan zargin jami’an ’yan sanda da hannu a ɓacewar Dadiyata.

Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Olatunji Disu, ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan wasu manyan jami’an ’yan sanda biyu bisa zargin alaƙarsu da ɓacewar fitaccen mai fafutuka a kafafen sada zumunta, Abubakar Idris Dadiyata.

Matakin ya biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da lauya kuma mai rajin kare haƙƙin ɗan Adam daga Kano, Abba Hikima, ya gabatar wa rundunar ’yan sanda, inda ya nemi a binciki zarge-zargen da ake yi wa CSP Hussaini Gimba da CSP Hassan Gimba.

Rahotanni sun bayyana cewa tsohon hadimin tsohon gwamnan Zamfara, Muhammad Musa Kamarawa, ya yi wasu ikirari da suka tayar da kura, inda ya ce jami’an sun taɓa faɗa masa cewa an kashe Dadiyata tare da wasu mutane a wani ofishin Operation Yaki da ke Kaduna.

A cikin ƙorafin da aka miƙa wa rundunar, an buƙaci a gudanar da sahihin bincike domin gano gaskiyar abin da ya faru, tare da tabbatar da cewa babu wanda doka za ta raina ko da yana da matsayi a gwamnati ko cikin jami’an tsaro.

Rundunar ’yan sanda ta tabbatar da cewa ta karɓi ƙorafin, sannan aka miƙa batun zuwa sashen kula da sa ido da binciken cikin gida domin fara aiki cikin gaggawa.

Masu fafutuka da al’umma dai sun dade suna neman bayani kan makomar Dadiyata, wanda aka yi garkuwa da shi daga gidansa da ke Barnawa a Kaduna tun watan Agustan shekarar 2019 ba tare da sake jin duriyarsa ba.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *