Shugaban rukunin kamfanonin BUA Group, AbdulSamad Rabiu, ya samu babban matsayi a nahiyar Afirka bayan da ya zama mutum na biyu mafi arziki a nahiyar.
Sabbin bayanai daga Bloomberg Billionaires Index sun nuna cewa attajirin ɗan kasuwar na Najeriya ya haura matsayi bayan ƙaruwa mai yawa da dukiyarsa ta samu a shekarar 2026.
Rahoton ya nuna cewa dukiyar Rabiu yanzu ta kai kusan dala biliyan 18.6, lamarin da ya ba shi damar wuce attajirin Afirka ta Kudu Johann Rupert, wanda aka ce dukiyarsa ta sauka zuwa dala biliyan 17.9.
Bloomberg ta bayyana cewa AbdulSamad Rabiu ne ya fi samun ƙarin arziki a Afirka a bana, musamman sakamakon ci gaban da kamfanoninsa ke samu a bangarorin siminti, masana’antu da harkokin abinci.
Sabon matsayin da Rabiu ya samu ya sanya shi kai tsaye bayan Aliko Dangote, wanda har yanzu yake ci gaba da riƙe kambun mutum mafi arziki a Afirka da kimanin dala biliyan 34.4.
Masana harkokin tattalin arziki na ganin wannan ci gaba alama ce ta yadda manyan ’yan kasuwar Najeriya ke ƙara faɗaɗa tasirinsu a nahiyar Afirka da ma duniya baki ɗaya.

