Kotu ta yankewa Alƙali hukunci dauri kan cin hancin Naira Miliyan 1 a Jihar Gombe.

Kotu ta yankewa Alƙali hukunci dauri kan cin hancin Naira Miliyan 1 a Jihar Gombe.

Babbar Kotun Jihar Gombe ta yanke wa wani Alƙali mai suna Mohammad Suleiman Kumo hukuncin ɗaurin shekaru biyu da rabi bayan samun sa da laifin karɓar cin hancin Naira miliyan ɗaya.
Mai shari’a Kereng, wanda ya jagoranci shari’ar, ya bayyana laifin a matsayin mai matuƙar tsanani, yana mai cewa kotun ta gamsu da hujjojin da aka gabatar a kansa.

Hukumar EFCC reshen Gombe ce ta gurfanar da Kumo a ranar 3 ga Disamba, 2025, kan tuhume-tuhume uku masu alaƙa da cin hanci da rashawa.

Binciken da aka gudanar ya nuna cewa yayin da yake aiki a matsayin Alƙalin Lardi a Pantami, ya karɓi Naira miliyan ɗaya ta hannun wani rajistara a kotunsa mai suna Adamu Ahmed ta asusun bankin Zenith a ranar 6 ga Nuwamba, 2024.

Tun farko dai Kumo ya musanta zarge-zargen da ake yi masa, amma daga baya lauyansa ya nemi kotu ta dakatar da shari’ar tare da miƙa lamarin ga Hukumar Kula da Ma’aikatan Shari’a ta ƙasa (JSC).

Sai dai masu gabatar da ƙara sun yi fatali da wannan buƙata, suna masu cewa wanda ake tuhuma ba ya cikin jami’an shari’ar da kundin tsarin mulki ya ware.

Kotun ta yi watsi da ƙorafin tare da tabbatar da cewa tana da ikon sauraron shari’ar.
A wani zaman kotu da aka gudanar ranar 5 ga Mayu, 2026, Kumo ya sauya matsayinsa tare da amsa laifin da ake tuhumarsa da shi bayan sake karanta tuhume-tuhumen a gabansa.

Daga nan ne kotu ta same shi da laifi tare da yanke masa hukuncin zaman gidan yari na shekaru biyu da rabi ko kuma ya biya tara ta Naira 250,000.

Haka kuma an umurce shi da ya biya EFCC Naira 500,000 a matsayin diyya kan kuɗaɗen bincike da shari’ar.
Rahotanni sun nuna cewa korafe-korafen wasu mutane biyu ne suka jawo fara binciken da ya kai ga gurfanar da alƙalin da kuma yanke masa hukunci.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *