Wata mummunar gobara da ta yi ajalin wasu mutum biyu ta kuma lalata bukkoki 200 a sansanin ‘yan gudun hijira da ke Bulabulin Damasak, a Jihar Borno.

Wata mummunar gobara da ta yi ajalin wasu mutum biyu ta kuma lalata bukkoki 200 a sansanin ‘yan gudun hijira da ke Bulabulin Damasak, a Jihar Borno.

Majiyoyin tsaro sun ce gobarar ta tashi ne a sansanin da ke ɗauke da mutane daga garuruwa sama da 10.

Rahotanni sun nuna cewa gobarar wadda ta riƙa yaɗuwa cikin sauri saboda yanayin bukkokin da aka yi wa rufi da ciyawa, ta yi sanadiyyar mutuwar mata biyu da ba a iya tantance su ba sakamakon yadda suka ƙone, yayin da wasu mutum biyar suka jikkata.

Jami’an tsaro tare da mazauna wurin sun yi ƙoƙarin kashe gobarar duk da rashin kayan aikin kashe gobara, amma dai hakan ya taimaka wajen hana ta yaɗuwa zuwa sauran sassan sansanin.

An kai waɗanda suka jikkata zuwa babban asibitin Damasak domin samun kulawa, inda aka tabbatar da mutuwar matan biyu, yayin da sauran ke ci gaba da karɓar magani.

Gobarar ta kuma lalata dukiyoyi na miliyoyin naira, yayin da har yanzu ba a gano musabbabin tashin ta ba.

An miƙa gawarwakin mamatan ga shugabannin al’umma domin yi musu jana’iza bisa koyarwar addinin Musulunci, yayin da ake ci gaba da bincike kan lamarin.

 

 

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *