Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta tabbatar da rasuwar wasu maniyyata aikin Hajji biyu a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da su.

Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta tabbatar da rasuwar wasu maniyyata aikin Hajji biyu a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da su.

Waɗanda suka rasu su ne Alkasim Ibrahim Walawa, mai shekara 48, da kuma mahaifiyarsa Hadiza Garba, mai shekara 73, dukkansu daga ƙauyen Walawa a Karamar Hukumar Kabo.

Rahotanni sun nuna cewa suna cikin shirin tafiye-tafiyen su na aikin Hajji zuwa Saudiyya ne lokacin da hatsarin ya rutsa da su.

A cewar hukumar, marigayin Alkasim ya bar mata biyu da ’ya’ya bakwai, yayin da mahaifiyarsa ta bar ’ya’ya biyar.

Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Sulaiman A. Dederi, ya bayyana cewa lamarin ya girgiza hukumar, kasancewar sun rasu ne a lokacin da suke shirin gudanar da ibada mai tsarki.

Hukumar ta yi addu’ar Allah Ya jikansu da rahama, Ya kuma sanya su a Aljannatul Firdaus, tare da jajanta wa iyalan da suka bari.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *