Rahoton daga shafin Open Treasury Portal ya bayyana cewa Rundunar Sojin Ƙasa ta samu kashi 7 kacal daga cikin kudin da aka ware domin sayen kayan tsaro, inda aka saki kusan Naira biliyan 1.46 daga cikin Naira biliyan 20.56. Haka kuma, a bangaren Rundunar Sojin Sama, an saki ƙananan kudade sosai idan aka kwatanta da abin da aka tsara, musamman wajen gyaran jiragen yaƙi.
Gaba ɗaya, bangarori da dama na tsaro kamar sayen kayan kare ƙasa, horar da jami’ai, da kula da kayan aiki sun samu ƙarancin kuɗi, yayin da wasu muhimman fannoni ba su samu ko sisi ba. Wannan ya haifar da damuwa kan yadda rundunonin tsaro za su iya tinkarar matsalolin tsaro da ke ƙara tsananta a faɗin ƙasar.
A lokaci guda, gwamnati ta tsawaita wa’adin aiwatar da kasafin 2025 zuwa tsakiyar 2026, matakin da ya ƙara jawo cece-kuce kan yadda ake tafiyar da kuɗaɗen ƙasa da kuma hauhawar bashin gwamnati.
Masana tsaro sun yi gargadin cewa wannan giɓin kuɗi na iya raunana ƙoƙarin yaƙi da ta’addanci da sauran laifuka, musamman a yankunan Arewa da ke fama da hare-hare. Rahotanni sun nuna cewa dubban mutane sun rasa rayukansu sakamakon rashin tsaro a cikin shekarar da ta gabata.
Haka kuma, an bayyana cewa rashin kayan aiki da isassun makamai na daga cikin manyan ƙalubalen da sojoji ke fuskanta a filin daga. Wasu jami’an gwamnati da ‘yan majalisa sun yi kira da a ƙara zuba jari a bangaren tsaro domin bai wa rundunonin ƙasa ƙarfin da suke buƙata.
A ƙarshe, masana da masu ruwa da tsaki sun jaddada cewa inganta tsarin kashe kuɗi, tabbatar da gaskiya da rikon amana, da kuma samar da kayan aiki na zamani su ne hanyoyin da za su taimaka wajen magance matsalar tsaro da ke addabar ƙasar.
