Hukumar shirya jarrabawar shiga jami’o’i ta ƙasa (JAMB) ta bayyana cewa ta kammala fitar da sakamakon UTME na shekarar 2026, wanda aka gudanar a ranakun 17 da 18 ga watan Afrilu.

Hukumar shirya jarrabawar shiga jami’o’i ta ƙasa (JAMB) ta bayyana cewa ta kammala fitar da sakamakon UTME na shekarar 2026, wanda aka gudanar a ranakun 17 da 18 ga watan Afrilu.

A cikin sanarwar da kakakin hukumar, Fabian Benjamin, ya fitar, hukumar ta ce sakamakon dalibai 1,264,940 na wadannan kwanaki biyu tuni an fitar da su domin al’umma su duba.

Hukumar ta kuma tunatar cewa an riga an fitar da sakamakon daliban da suka rubuta jarabawa a ranar Alhamis 16 ga Afrilu.

JAMB ta shawarci dalibai da su duba sakamakon su ta hanyar amfani da SMS na hukumar.

Inda ta ce sakamakon da aka fitar ya shafi kwanaki uku ne na farko na jarabawar a faɗin ƙasa baki ɗaya.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *