Kungiyar  Boko Haram ta sake kai hari garin Benishiekh a Jihar Borno.

Kungiyar Boko Haram ta sake kai hari garin Benishiekh a Jihar Borno.

Rahotanni daga jihar Borno na nuna cewa ’yan ta’addan Boko Haram sun sake kai wani hari a garin Benishiekh, wanda ke kan babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu, a karo na biyu cikin ƙasa da mako guda.

Lamarin ya ƙara tayar da hankalin mazauna yankin, musamman ganin yadda maharan ke karkata akalarsu zuwa sansanin rundunar sojoji ta 29 na Operation Hadin Kai. Wannan dai shi ne wurin da aka kashe Birgediya Janar O.O. Braimah a makon da ya gabata.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa an hango wasu daga cikin ’yan ta’addan suna yawo a wasu sassan garin, abin da ya ƙara tsoratar da jama’a.

Haka kuma, majiyoyi sun ce a ’yan kwanakin baya an lura da wasu mutane da ake zargi da alaka da ’yan ta’addan suna zirga-zirga da babura a kusa da yankin. A cewar wata majiya daga cikin al’umma, irin wannan motsi na iya zama alamar shirin kai hari da daddare, inda maharan ke barin baburansu a nesa kafin su shiga cikin gari.

Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar Operation Hadin Kai, Laftanar Janar Sani Uba, kan lamarin bai yi nasara ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

 

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *