
Tsohon mataimakin Gwamnan Kano kuma dan takarar Gwamna a Jamiyyar APC a zaben 2023 daya gabata Dr Nasiru Yusuf Gawuna yayi murabus daga mukamin sa na Shugaban Gudanarwa Bankin bada lamunin gidaje na kasa (Federal Mortgage Bank).
Hakan na zuwa ne a yau Litinin inda ake kyautata zaton zai fice daga Jamiyyar APC domin karbar Shahadar Kwankwasiyya karkashin Jagorancin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Tunda farko dai a kwanakin baya anjiyo wasu kungiyoyi da suke da alaka dashi suna ta kira gare shi daya kwashe su ya kaisu wajen Kwankwaso, wanda daga nisani suka canza salo na cewa a zare bulo 8 su shiga gidan Kwankwaso.
A yau ne ake sa ran Kwankwason zai koma Jamiyyar ADC da misalin karfe 12 na rana a gidan sa dake mila road a kano.
Shin kuna ganin Gawunan zaibi Kwankwason ne ko kuma Aa.