Ana sa ran komawar tsohon gwamnan jihar Kano Sen Rabi’u Musa Kwankwaso jam’iyar ADC a yau litinin

Ƙungiyoyin siyasa na tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso da kuma na ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party a zaɓen shekarar 2023, Peter Obi, sun tabbatar da cewa ana ci gaba da tattaunawa wadda za ta iya kaiwa ga haɗa tikitin takarar shugaban ƙasa na bai ɗaya tsakanin shugabannin biyu gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Ana sa ran tsohon gwamnan jihar Kano zai sanar da shiga jam’iyyar ADC a yau Litinin, inda shugaban jam’iyyar na ƙasa David Mark da sakatarenta na ƙasa Rauf Aregbesola za su karɓe shi a hukumance.

Ana kuma sa ran zai shiga jam’iyyar tare da tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, Conrade Aminu Abdussalam Gwarzo.

Kafin wannan sauya sheƙa ta siyasa, a ƙarshen makon da ya gabata Kwankwaso ya kai ziyara ga tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar a birnin Abuja, bayan wata ganawa da ya yi tun da farko da Rauf Aregbesola.

Tun da farko kuma Kwankwaso ya karɓi baƙuncin Obi a lokacin bikin Durbar na Sallah da aka gudanar a Kano, inda suka je tare da gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, da kuma tsohon gwamnan jihar Bayelsa, Seriake Dickson.

Wannan lamari ya zo ne bayan da Kwankwaso ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar NNPP a ranar Lahadi, yana mai cewa ya ɗauki wannan mataki ne saboda buƙatar sake tsara tafiyar siyasa

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *