
Ministan Makamashi, Bayo Adelabu, ya roƙi ’yan Najeriya da su yi haƙuri dangane da ƙarancin wutar lantarki da ake fama da shi a sassa daban-daban na ƙasar.
Ministan ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja, inda ya amince da cewa matsalar wutar ta jima tana addabar al’umma.
A cewarsa, matsalolin da suka dabaibaye fannin samar da lantarki sun yi tsanani matuƙa, kuma ba za a iya magance su cikin ɗan gajeren lokaci ba.
Ya ƙara da cewa waɗannan ƙalubale sun haɗa da matsalolin da suka shafi samarwa, rarrabawa da kuma kula da kayayyakin lantarki, lamarin da ya janyo tangarɗa a wadatar wutar lantarki.
Sai dai duk da haka, Ministan ya yi alƙawarin cewa gwamnati na ɗaukar matakai domin gyara wannan hali, yana mai jaddada cewa nan gaba kaɗan za a fara samun sauƙi.
Ya kuma bayyana cewa gwamnati na fatan kafin ƙarshen shekarar nan za a samu ingantacciyar wadatar wutar lantarki a faɗin Najeriya.