Ɗimbin masunta sun rasa rayukansu sakamakon wani hari ta sama da rundunar sojin Chadi ta kai a yankin Tafkin Chadi.

Ɗimbin masunta sun rasa rayukansu sakamakon wani hari ta sama da rundunar sojin Chadi ta kai a yankin Tafkin Chadi.

Bayanan da ke fitowa daga yankin sun nuna cewa mafi yawan waɗanda harin ya rutsa da su ’yan Najeriya ne da ke gudanar da sana’ar kamun kifi a wasu tsibirai da ke kusa da iyakokin Najeriya da Nijar.

Harin ya zo ne bayan mayaƙan Boko Haram sun kai farmaki a wani sansanin sojin Chadi tare da kashe dakaru da dama, abin da ya sa hukumomin ƙasar suka ƙaddamar da martani ta sama domin kai hare-hare kan wuraren da ake zargin mayaƙan na fakewa.
Mazauna yankin da masu aikin sa-kai sun ce an kai hare-haren tun daga ranar Juma’a, kuma an samu asarar rayuka masu yawa duk da cewa ba a tantance adadin mamatan ba tukuna.

Wasu daga cikin mazauna yankin sun bayyana cewa masuntan da aka kashe na gudanar da sana’arsu ne bayan samun izini daga mayaƙan Boko Haram, waɗanda ke karɓar haraji daga masu kamun kifi a yankin.
Haka kuma, wani shugaban al’umma daga Tsibirin Shuwa ya bayyana cewa akwai mutane da dama da har yanzu ba a gano su ba bayan harin, lamarin da ke ƙara jefa iyalansu cikin fargaba.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *