Wani tsagin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ƙarƙashin jagorancin Shugabanta na Ƙasa, Nafiu Bala Gombe, ya yi fatali da rahotannin da ke yaɗuwa cewa tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, shi ne ɗan takarar shugaban ƙasar jam’iyyar a babban zaɓen shekarar 2027.
A wata sanarwa da ya fitar, Gombe ya bayyana cewa Atiku bai taɓa samun takarar shugaban ƙasa ta jam’iyyar ADC ba, yana mai cewa jam’iyyar ta bi dukkan matakan da kundin dokokinta da kuma dokokin zaɓe suka tanada wajen zaɓen ɗan takara.
Ya ce bayan kammala waɗannan matakai, jam’iyyar ta amince da Farfesa Chris Uba a matsayin wanda zai wakilce ta a takarar shugaban ƙasa.
Tsagin ya kuma yi watsi da duk wata alaƙa da wata ƙungiya da ake dangantawa da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark, yana mai cewa ƙungiyar ba ta da wata sahihiyar matsayi a cikin tsarin jam’iyyar ADC.
A cewar Gombe, ƙungiyar ba ta da ikon gudanar da zaɓen fidda gwani ko yanke hukunci a madadin jam’iyyar, domin ba ta cikin halastattun hukumomin da ke tafiyar da harkokin ADC.
Ya kuma jaddada cewa jam’iyyar ba ta shiga wata haɗaka ko yarjejeniyar siyasa da kowace jam’iyya ba, yana mai cewa ADC za ta shiga zaɓen 2027 ne bisa manufofinta da tsare-tsarenta na siyasa.
Shugaban tsagin ya gargadi Atiku Abubakar da ya guji bayyana kansa a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, yana mai cewa jam’iyyar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen amfani da hanyoyin doka domin kare mutuncinta da tsarin gudanarwarta.
Haka kuma, ya yi watsi da zarge-zargen da ke cewa akwai wani yunƙuri na hana jam’iyyar shiga zaɓen shekarar 2027, yana mai nuna cikakken amincewa da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da kuma tsarin dimokuraɗiyyar Najeriya.
A ƙarshe, tsagin ya bayyana cewa ADC na ci gaba da shirye-shiryen fuskantar zaɓukan 2027, tare da aniyar tsayar da ’yan takara da take ganin za su iya jagorantar ƙasa a matakai daban-daban na gwamnati.

