Sojoji sun kuɓutar da matar marigayi Janar Rabe daga hannun ’yan bindiga

Sojoji sun kuɓutar da matar marigayi Janar Rabe daga hannun ’yan bindiga

Dakarun sojin Najeriya sun yi nasarar ceto Hajiya Amina Abubakar, matar marigayi Manjo Janar Rabe Abubakar, bayan ta shafe lokaci a hannun masu garkuwa da mutane.

Rahotanni sun nuna cewa rundunar Operation FANSAN YANMA ce ta gudanar da aikin ceton bayan wani samame da aka kai kan maɓoyar ’yan bindiga a yankin Ƙaramar Hukumar Matazu ta Jihar Katsina.

Bayanan tsaro sun bayyana cewa an kai farmakin ne a ƙarƙashin shirin Operation CLEAN SWEEP III, bayan samun bayanan sirri da suka taimaka wajen gano inda aka tsare matar.

A yayin aikin ceton, sojojin sun yi musayar wuta da maharan a ƙauyen Tunga. An ce matsin lambar da dakarun suka yi ya sa ’yan bindigar suka harbi Hajiya Amina kafin su tsere zuwa cikin daji.

Wata majiya daga bangaren tsaro ta ce an same ta da raunin harsashi, inda aka ba ta kulawar gaggawa nan take kafin a kai ta asibiti domin ci gaba da jinya.

Majiyar ta ƙara da cewa halin da take ciki na samun kulawa daga jami’an lafiya, yayin da ake sa ran za ta ci gaba da murmurewa.

A halin yanzu, sojoji sun ce suna ci gaba da bibiyar maharan da suka tsere tare da ƙara ƙaimi wajen gano da kuma cafke duk masu hannu a hare-haren da sace-sacen mutane da ke addabar yankin.

Rundunar ta kuma tabbatar da cewa hare-haren da take kai wa maɓoyar ’yan bindiga a ƙarƙashin Operation CLEAN SWEEP III za su ci gaba har sai an lalata sansanonin masu aikata laifukan gaba ɗaya.

Jami’an tsaro sun sake jaddada aniyarsu ta tabbatar da cewa an kamo duk waɗanda ke da hannu a wannan hari domin su fuskanci hukuncin da doka ta tanada.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *