Gwamnatin Jihar Katsina ta dakatar da harkokin POS,  da cajin waya a wasu yankuna.

Gwamnatin Jihar Katsina ta dakatar da harkokin POS, da cajin waya a wasu yankuna.

Gwamnatin Jihar Katsina ta sanar da haramta gudanar da sana’ar POS, cajin wayoyi da kuma haya babur a Ƙananan Hukumomin Matazu da Musawa, a wani mataki da ta ce an ɗauka domin ƙarfafa yaƙi da matsalar tsaro a yankunan.

Haka kuma, gwamnatin ta kafa dokar hana sayarwa ko jigilar man fetur a cikin jarkoki a duk faɗin jihar, tana mai cewa matakin zai taimaka wajen hana isar da man ga masu aikata ta’addanci da ke ɓoye a dazuka.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata dokar zartarwa da Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa ya amince da ita, bayan wata ganawa ta musamman da jami’an tsaro, sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki kan matsalar tsaro a jihar.

A cewar Babban Sakataren Yaɗa Labaran Gwamnan Jihar, Ibrahim Kaula Mohammed, bayanan sirri da rahotannin bincike sun nuna cewa wasu masu aikata laifuka na amfani da cibiyoyin POS da wuraren cajin waya wajen gudanar da mu’amalolinsu da sadarwa.

Ya ƙara da cewa hana safarar fetur a cikin mazubai na daga cikin matakan da gwamnati ke ɗauka domin toshe hanyoyin da ake amfani da su wajen kai kayan masarufi da makamashi zuwa maɓoyar ’yan bindiga.

Sanarwar ta ce binciken hukumomin tsaro ya kuma gano cewa wasu daga cikin wuraren hada-hadar kuɗi da cajin wayoyi na taka rawa wajen sauƙaƙa ayyukan masu laifi, lamarin da ya sa aka ba da umarnin rufe su a yankunan da abin ya shafa.

Bugu da ƙari, an dakatar da harkar haya da babura a Matazu da Musawa saboda zargin cewa masu garkuwa da mutane da ’yan bindiga na amfani da su wajen zirga-zirga da gudanar da ayyukansu.

Gwamna Raɗɗa ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ɗaukar duk matakan da suka dace domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a tare da haɗa kai da hukumomin tsaro wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Ya kuma yi kira ga al’umma da su mutunta sabbin dokokin tare da ci gaba da bai wa jami’an tsaro bayanan da za su taimaka wajen yaƙi da miyagun laifuka.

Gwamnan ya yi gargadin cewa duk wanda aka samu da karya dokar zartarwar zai fuskanci hukuncin da doka ta tanada, yana mai jaddada cewa gwamnati ba za ta lamunci duk wani yunƙurin karya doka ba.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *