Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta sanar da karɓar wasu ‘yan Najeriya 123 da aka dawo da su daga ƙasar Aljeriya a wani ɓangare na shirin mayar da ‘yan ƙasar da suka maƙale a ƙasashen waje zuwa gida.
A cewar hukumar, mutanen sun iso tashar Cargo Terminal da ke Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed a Ikeja, Jihar Legas, cikin jirgin Nesma Airlines a ranar Litinin.
NEMA ta bayyana cewa aikin karɓar mutanen ya gudana ne tare da haɗin gwiwar Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira, Masu Ƙaura da Mutanen da Rikici ya Raba da Muhallansu (NCFRMI), da kuma sauran hukumomin gwamnati masu ruwa da tsaki domin tabbatar da dawowarsu cikin aminci da mutunci.
Bayanan da hukumar ta fitar sun nuna cewa daga cikin mutanen 123 da aka dawo da su akwai manya 121, waɗanda suka haɗa da maza 112 da mata tara. Haka kuma akwai yarinya guda ɗaya da jariri namiji guda ɗaya.
NEMA ta tunatar da cewa a watan Yulin 2025 ma ta karɓi wasu ‘yan Najeriya 104 da suka dawo daga Aljeriya. A lokacin, adadin ya ƙunshi maza manya 80, mata manya 14, yara maza biyu, yara mata biyar da kuma jarirai uku.
Hukumar ta ce bayan isowarsu, ana gudanar da rajista da tantance bayanai ta hannun Hukumar Shige da Fice ta Najeriya, sannan a samar musu da tallafin jin ƙai da ya haɗa da abinci, ruwan sha, kulawar lafiya da kuma taimakon sufuri domin sauƙaƙa musu komawa cikin al’umma.

