Gwamnatin Tarayya na shirin haɗa JSS da SSS domin rage yawan yaran da ke ficewa daga makaranta

Gwamnatin Tarayya na shirin haɗa JSS da SSS domin rage yawan yaran da ke ficewa daga makaranta

Gwamnatin Tarayya ta bayyana aniyarta ta kawo ƙarshen tsarin raba ƙananan makarantun sakandire (JSS) da manyan makarantun sakandire (SSS), a wani yunkuri na inganta harkar ilimi da kuma rage yawan ɗaliban da ke daina karatu kafin su kammala matakin sakandire.

Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ya bayyana hakan ne a Abuja yayin ƙaddamar da Kwamitin Kula da Aiwatarwa da Bibiyar Ayyukan Hukumar Ilimin Bai Ɗaya ta Ƙasa (UBEC).

A cewarsa, bayanan da gwamnati ta tattara sun nuna cewa sama da ɗalibai miliyan 20 ne ke barin makaranta kafin su kai matakin babbar sakandire, lamarin da ya sa ake duba yiwuwar sauya tsarin da ake amfani da shi a yanzu.

Alausa ya bayyana cewa tsarin raba JSS da SSS tare da ware musu shugabanni da kayan aiki daban-daban bai samar da sakamakon da aka yi fata ba. Ya ce hakan ya haddasa cunkoso a wasu makarantun JSS, yayin da makarantun SSS da dama ke fama da rashin cikakken amfani da kayayyakin da aka tanada musu.

Ya nuna Jihar Kaduna da wasu jihohin Arewa a matsayin misalan wuraren da ake fuskantar irin wannan matsala, inda ake samun rashin daidaito wajen amfani da kayan more rayuwa na makarantu.

Ministan ya ce za a gabatar da wannan shawara ta soke tsarin raba JSS da SSS a zama na gaba na Majalisar Ilimi ta Ƙasa domin yin nazari da yanke hukunci a kai.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *