Matakin nasa ya jawo hankali musamman saboda alakarsa da tafiyar Kwankwasiyya duk da cewa mahaifinsa na daga cikin manyan jiga-jigan APC a Najeriya.
Rahotanni sun nuna cewa Abdulaziz ya sayi fom ɗin takarar ne sannan daga bisani ya gana da tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, inda suka tattauna kan shirinsa na shiga zaɓe mai zuwa.
Wani bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta ya nuna lokacin ganawar tasu, lamarin da ya sake nuna yadda Abdulaziz ke ci gaba da kusanci da Kwankwaso duk da dambarwar siyasa tsakanin Kwankwaso da Ganduje.
Tun da dadewa Abdulaziz ke bayyana ra’ayinsa na goyon bayan tafiyar Kwankwasiyya, lamarin da ya bambanta shi da siyasar mahaifinsa.
Haka kuma, a baya an taɓa samun rashin jituwar iyali tsakaninsa da mahaifiyarsa, Farfesa Hafsat Ganduje, inda har aka kai batun ga hukumar EFCC.
Ana sa ran Abdulaziz zai fafata ne kan kujerar Majalisar Tarayya da ɗan uwansa ya nema a zaɓen 2023 ƙarƙashin APC amma bai samu nasara ba bayan ɗan takarar NNPP ya kayar da shi duk da kasancewar Ganduje na mulkin Kano a lokacin.
