Gwamna Abba Kabir Yusuf ya buƙaci ƙara ƙarfafa haɗin gwiwar Kano da Faransa.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya buƙaci ƙara ƙarfafa haɗin gwiwar Kano da Faransa.

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya taya gwamnati da al’ummar ƙasar Faransa murnar zagayowar Ranar Ƙasar Faransa, tare da sake jaddada aniyar gwamnatin jihar na ƙara ƙarfafa alaƙar haɗin gwiwa da ƙasar a muhimman fannoni na ci gaba.

Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Darakta Janar na Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Gidan Gwamnatin Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Talata.

Gwamna Yusuf ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da aka gudanar a Ofishin Jakadancin Faransa da ke Abuja domin bikin Ranar Ƙasar Faransa, inda ya jagoranci tawagar manyan jami’an gwamnatin Kano zuwa taron.

A jawabinsa, gwamnan ya miƙa saƙon taya murna ga Jakadan Faransa a Najeriya, Mai Girma Marc Fonbaustier, a madadin gwamnati da al’ummar Jihar Kano, tare da yi wa ƙasar fatan ci gaba da zaman lafiya, wadata da cigaba.

Ya yaba da daɗaɗɗiyar alaƙar da ke tsakanin Najeriya da Faransa, yana mai cewa wannan haɗin gwiwa ya taimaka wajen bunƙasa ci gaba da ƙarfafa fahimtar juna tsakanin ƙasashen biyu.

Gwamnan ya kuma buƙaci a ƙara faɗaɗa haɗin gwiwa tsakanin Jihar Kano da gwamnatin Faransa musamman a fannoni kamar noma, makamashi mai sabuntawa, albarkatun ruwa, kare muhalli da ilimi.

A cewarsa, gwamnatin Kano za ta ci gaba da aiki tare da ƙasashen duniya da sauran abokan hulɗa domin jawo masu zuba jari, inganta ayyukan gwamnati da kuma kyautata rayuwar al’ummar jihar.

Ya bayyana kwarin gwiwar cewa ƙarfafa alaƙa da Faransa zai samar da sabbin damammaki a fannonin fasaha, musayar ilimi da ƙwarewa, da kuma bunƙasa ci gaba mai ɗorewa a Jihar Kano.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *