Wasu mahara sun kai hari a wata makaranta dake garin Lassa a Jihar Borno

Wasu mahara sun kai hari a wata makaranta dake garin Lassa a Jihar Borno

Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA) ta bayyana matuƙar damuwarta kan harin da aka kai wata makaranta a garin Lassa da ke Ƙaramar Hukumar Askira/Uba a Jihar Borno, wanda ya yi sanadin kashe wani malami tare da sace ɗalibai da malamai.

A wata sanarwa da ta fitar ta hannun jami’in hulɗa da jama’a, Abbas Jimoh, majalisar ta ce harin wani abin takaici ne da ke nuna cewa har yanzu matsalar tsaro na ci gaba da barazana ga rayuka da ilimin yara a yankin Arewa maso Gabas.

Ƙarƙashin jagorancin Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, majalisar ta bayyana cewa hare-haren da ake kai wa makarantu na da illa ga makomar matasa da ci gaban ƙasa baki ɗaya, don haka akwai buƙatar ɗaukar ƙarin matakan kariya.

NSCIA ta lura cewa wannan hari ya biyo bayan wani makamancin lamari da ya faru a baya-bayan nan, inda aka yi garkuwa da ɗalibai da dama, lamarin da ke nuna buƙatar sake duba dabarun tsaro a wuraren ilimi.

Majalisar ta yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su ƙara amfani da bayanan sirri, tsarin sa ido da haɗin gwiwa da al’umma wajen gano barazana tun kafin ta afku.

Ta kuma yabawa dakarun Operation HADIN KAI bisa nasarar da suka samu wajen ceto wasu daga cikin mutanen da aka sace, tana mai buƙatar a ci gaba da ƙoƙarin neman sauran waɗanda har yanzu ba a kuɓutar da su ba.

Haka kuma, majalisar ta miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan jami’in soja da ɗan ƙungiyar Civilian JTF da suka rasa rayukansu yayin aikin ceto, tana mai yabawa jajircewarsu wajen kare jama’a.

A ƙarshe, NSCIA ta sake jaddada cewa ayyukan Boko Haram da ISWAP sun saɓa wa koyarwar Musulunci da ƙa’idodin zaman lafiya, tana mai kira da a ci gaba da yaƙi da ta’addanci domin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a Najeriya.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *