Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tura wata tawaga ta manyan jami’an gwamnati zuwa yankin Ogbomoso na Jihar Oyo bayan harin da ya yi sanadin sace ɗalibai da malamai kusan 46 daga wasu makarantu biyu.
Tawagar da shugaban ƙasar ya aike ta haɗa da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu, da Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Tunde Disu.
Haka kuma tawagar ta ƙunshi Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa, Ministan Wutar Lantarki, Joseph Tegbe, da Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Hulɗa da Jama’a, Sunday Dare.
Matakin ya biyo bayan hare-haren da wasu da ake zargin ’yan ta’adda ne suka kai lokaci guda a Makarantar Baptist Nursery da Primary School da ke ƙauyukan Esiele da Yawota, inda suka yi awon gaba da ɗalibai da malamai da dama.
Rahotanni sun ce bayan aukuwar lamarin, Shugaba Tinubu ya ba hukumomin tsaro umarnin gaggauta ɗaukar matakan da suka dace domin ceto waɗanda aka yi garkuwa da su tare da kamo waɗanda suka aikata laifin.
Duk da ƙoƙarin da jami’an tsaro ke yi, har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto ba a samu nasarar kuɓutar da mutanen da aka sace ba, yayin da iyalai da al’ummar yankin ke ci gaba da jiran sakamakon ayyukan ceto.
