Sakamakon zaben ya nuna cewa Nalaraba, mai wakiltar mazabar Awe/Doma/Keana a majalisar wakilai, ya samu kuri’u 48,482, yayin da Akabe ya tsaya kan kuri’u 32,881.Musa Shuaibu Guri, shugaban kwamitin zaben, shi ne ya bayyana sakamakon tare da tabbatar da cewa Nalaraba ya zama wanda zai wakilci APC a zaben Sanata mai zuwa.
Akabe, wanda ya taba zama dan Majalisar Wakilai kafin hawansa kujerar mataimakin gwamna, ya shiga takarar ne da fatan samun damar komawa majalisar dokoki ta kasa, amma bai samu goyon bayan da ya kai shi ga nasara ba.Haka kuma, bayan Nalaraba ya samu tikitin takarar Sanata, APC ta gudanar da zaben fid-da gwani domin nemo wanda zai maye gurbinsa a mazabar Awe/Doma/Keana.
A wannan zabe, Yakubu Dalhatu Araf ne ya fito da nasara bayan samun kuri’u 20,661, inda ya doke sauran ’yan takarar da suka fafata da shi.

