Majiyoyi masu ƙarfi sun bayyana cewa maharan sun ƙi yin magana da iyalan waɗanda aka sace, inda suka ce suna son yin magana ne kai tsaye da gwamnan jihar kaɗai domin tattaunawa.
Majiyoyin sun ce har yanzu ba a san cikakken abin da maharan suke nema ba, saboda ana ɓoye bayanan tattaunawar domin kare rayukan waɗanda aka sace. Haka kuma, ba a tabbatar ko gwamnan jihar ne da kansa ke jagorantar tattaunawar ko kuma wani wakilinsa ne yake yi.
Wata majiya ta bayyana cewa bude hanyar sadarwa tsakanin gwamnati da maharan ya kawo ɗan kwanciyar hankali, duk da cewa jami’an tsaro suna cikin ƙalubale saboda haɗarin da ke tattare da aikin ceto. Mai bai wa gwamna shawara kan harkokin tsaro, Abayomi Fagbenro, ya ƙi yin karin bayani kan lamarin a wannan lokaci.

