Lamarin, wanda ya faru ranar Talata, ya haifar da ce-ce-ku-ce inda ‘yan Najeriya da dama suka zargi hukumar da amfani da ƙarfi da wuce gona da iri.
Haka kuma, manyan lauyoyi da ƙungiyoyin farar hula da suka tattauna da jaridar Saturday PUNCH sun yi kira da a sake fasalin yadda hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ke gudanar da ayyukanta.
EFCC na ci gaba da fuskantar suka bayan jerin samame masu tada ƙura da ta kai kan gidaje, otal-otal, dakunan kwanan ɗalibai da wasu cibiyoyi yayin gudanar da ayyukan kama waɗanda ake zargi da aikata laifukan kuɗi, musamman damfara ta intanet.

