Tun da farko, Mahmud Sadis ya bayyana aniyarsa ta neman wakiltar mazabar Sabon Gari ta Jihar Kaduna a Majalisar Tarayya ƙarƙashin Jam’iyyar APC, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta da na watsa labarai.
A cikin wasiƙar da ya aikewa shugaban APC na Jihar Kaduna, ya bayyana cewa ya janye takarar ne domin bai wa yunƙurin sasanta rikice-rikicen cikin gida da shugabannin jam’iyyar ke yi dama.
Janyewar tasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta muhawara kan ainihin shekarunsa, bayan wasu rahotanni sun nuna cewa an haife shi ne a watan Agustan shekarar 2010.
Idan har hakan gaskiya ne, hakan na nuna cewa shekarunsa ba su kai mafi ƙarancin shekarun da kundin tsarin mulki ya tanada ga masu neman kujerar Majalisar Tarayya ba.
Abin Al’ajabi ya fara jan hankalin jama’a ne bayan wani bidiyo ya nuna lokacin da ya kai fom ɗinsa na neman takara zuwa ofishin APC.
A lokacin tantancewa, ya bayyana cewa mutanen mazabarsa ne suka roƙe shi da ya tsaya takara domin wakiltarsu.
Da aka tambaye shi game da shekarunsa, ya ce ya wuce shekara 25, sannan ya bayyana cewa ya kammala karatun sakandare tare da gabatar da sakamakon jarabawar NECO.
Bayan haka kuma, hotunansa tare da manyan shugabannin APC ciki har da Shugaba Bola Tinubu da shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio da Gwamnan Kaduna Uba Sani suka bazu a kafafen sada zumunta.

