Aƙalla mutum 10 ne suka rasa rayukansu bayan da wasu ’yan bindiga suka kai hari kan ayarin matafiya a Jihar Zamfara

Aƙalla mutum 10 ne suka rasa rayukansu bayan da wasu ’yan bindiga suka kai hari kan ayarin matafiya a Jihar Zamfara

Harin ya auku ne a yammacin ranar Lahadi a kan hanyar Magami zuwa Ɗansadau, inda matafiya suka shiga cikin firgici tare da guduwa zuwa dazuka domin tsira da rayukansu.
Wani mazaunin yankin mai suna Malam Aliyu ya bayyana cewa matafiyan sun daɗe suna jiran rakiyar jami’an tsaro kafin daga bisani su fara tafiya, sai dai ’yan bindigar suka kai musu hari a yankin Dogon Santsi.
A cewarsa, maharan sun farmaki jami’an tsaron da ke rakiyar ayarin tare da kashe wasu daga cikin jami’an, fararen hula da kuma mambobin kungiyar CJTF, yayin da wasu da dama suka samu raunuka.
Ya ƙara da cewa an tabbatar da mutuwar mutum 10, yayin da ake ci gaba da neman wasu da suka ɓace bayan harin.
Shi ma wani matafiyi da ya tsira daga harin, Aminu Muhammad, ya ce bayan harin ne aka jira ƙarin jami’an tsaro kafin a kai waɗanda suka jikkata zuwa Gusau domin samun kulawar likitoci.
Aminu ya kuma yi zargin cewa maharan sun yi awon gaba da wasu matafiya, duk da cewa ba a tantance adadinsu ba har yanzu.
Duk da haka, ya yaba wa jami’an tsaro bisa ƙoƙarin da suke yi wajen kare lafiyar matafiya a yankin.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, rundunar ’yan sandan Zamfara ba ta fitar da wata sanarwa ba kan harin, domin kakakin rundunar bai amsa saƙonnin neman bayani da aka aike masa ba

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *