Kwamishinan Ilimi na jihar, Dakta Ali Haruna Makoda, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a Kaduna. Ya ce an cafke wasu daga cikin ma’aikatan da suka karɓi kuɗi daga hannun jama’a tare da yi musu alkawarin samar musu da takardun daukar aiki.
Ya kuma bukaci duk wanda ya biya kudi domin samun irin wannan takarda da ya gaggauta kai rahoto zuwa ofishinsa, tare da bayyana sunan wanda ya karɓi kudin domin daukar mataki.
Dakta Makoda ya jaddada cewa ma’aikatar ba za ta amince da duk wani yunkuri na kawo cikas ga shirin gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf na farfaɗo da ilimi a jihar ba. Ya ce duk wanda aka samu da hannu a irin wannan badakala zai fuskanci hukunci mai tsauri.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ma’aikatar ilimi ke ci gaba da raba takardun daukar aiki ga sabbin malaman firamare, bayan umarnin gwamnan jihar na daukar karin malamai domin magance karancin ma’aikata a makarantun firamare.

