Matsalar Tsaro a Najeriya wasu ne suke yiwa shugaba Tinbu zagon kasan – Akpabio.

Matsalar Tsaro a Najeriya wasu ne suke yiwa shugaba Tinbu zagon kasan – Akpabio.

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Godswill Akpabio, ya bayyana cewa matsalar tsaro da ke ƙara kamari a ƙasar nan wata maƙarkashiya ce da ake kitsa wa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Ya yi wannan furuci ne a ranar Talata a Abuja, yayin kaddamar da sabuwar hedikwatar Hukumar Haraji ta ƙasa.

Akpabio ya ce masu ɗaukar nauyin hare-haren tsaro na ƙoƙarin karkatar da hankalin shugaban ƙasa daga sauye-sauyen da yake aiwatarwa.

A cewarsa, “Ina tabbatar maka, Shugaban ƙasa, makonni biyu bayan ka ci zaɓe, hare-haren bam za su daina. Akwai waɗanda ke ɗaukar nauyin waɗannan hare-hare domin janye hankalinka daga ayyukan da kake yi.”

Kalaman nasa na zuwa ne ƙasa da sa’o’i 24 bayan wata ganawar sirri da aka ce Shugaba Tinubu ya yi da babban hafsan tsaro, Janar Olufemi Oluyede, tare da wani babban jami’in sojin Faransa a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Majiyoyi na kusa da fadar shugaban ƙasa sun bayyana ganawar a matsayin wani mataki na ƙarfafa dabarun magance matsalar tsaro da ke ƙara ta’azzara a ƙasar.

Haka kuma, an ce wannan na zuwa ne makonni uku bayan shugaban ƙasa ya sanar da cewa ƙasar Faransa ta amince da tallafa wa Najeriya da kayan aikin soja da kuma horas da jami’an tsaro domin yaƙi da ’yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabas.

Wannan bayani na Akpabio ya zo ne a daidai lokacin da ake fuskantar matsalolin tsaro a sassa daban-daban na ƙasar, ciki har da harin jirgin saman yaƙi na rundunar sojin sama da ya kashe fararen hula sama da 100 a kasuwar Jilli da ke jihar Borno—hari da hukumomi suka ce an kai shi ne bisa kuskure.

Haka zalika, akwai matakin da Amurka ta ɗauka na janye wasu ma’aikatan ofishin jakadancinta da ba su da muhimman ayyuka daga Abuja, sakamakon damuwar tsaro.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *