Wata Kotu a Jihar  Gombe ta yankewa wani Matashi Hukuncin Kisa ta hanyar Rataya bayan samun sa da laifin aikata Kisan Kai.

Wata Kotu a Jihar Gombe ta yankewa wani Matashi Hukuncin Kisa ta hanyar Rataya bayan samun sa da laifin aikata Kisan Kai.

Babbar Kotun Jihar Gombe mai lamba 2 ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wani matashi mai shekaru 18, Mustapha Adamu Isah, wanda aka fi sani da Abbati, bayan samun sa da laifin kashe wata mata mai shekaru 58, Aishatu Abdullahi (Damori).

Mai shari’a Abdulhamid Mohammed Yakubu ne ya yanke hukuncin, inda ya bayyana cewa an tabbatar da laifin da ake tuhumar wanda ake zargi da shi ba tare da wata shakka ba.

Kotun ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar 20 ga Oktoba, 2023, da misalin karfe 9:00 na dare a unguwar Jekadafari da ke cikin birnin Gombe.

Rahotanni sun nuna cewa matashin, wanda ke zaune a titin Santana, ya shiga gidan marigayiyar ba bisa ka’ida ba, inda ya kai mata hari da wuka, wanda hakan ya yi sanadin rasuwarta.

Daraktan Sashen Gurfanar da Kara na gwamnati, Barista Abubakar Jungudo, ya bayyana cewa laifin ya saba wa Sashe na 220 na Dokar Penal Code, wanda hukuncinsa ke karkashin Sashe na 221.

Duk da cewa wanda ake tuhuma ya musanta zargin, masu gabatar da kara sun gabatar da hujjoji da shaidu da suka tabbatar da aikata laifin.

Lauyan wanda ake tuhuma, Barista Adamu Abdulkadir, ya yi kokarin kalubalantar shaidun da aka gabatar, amma kotu ta dogara da bayanai da hujjojin da aka gabatar wajen yanke hukunci.

A karshe, kotu ta same shi da laifi tare da yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya kamar yadda doka ta tanada.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *