Ana zargin wano Tsoho da yin lalata da Jikarsa har ta kai ta da yin ciki.

Ana zargin wano Tsoho da yin lalata da Jikarsa har ta kai ta da yin ciki.

Wani lamari mai tayar da hankali ya faru a Jihar Neja, inda jami’an ’yan sanda suka tsare wani tsoho bayan gwajin DNA ya tabbatar da cewa shi ne mahaifin jaririn da jikarsa mai shekaru 16 ta haifa.

Rahotanni sun nuna cewa mutumin ya dade yana lalata da yarinyar, lamarin da ya kai ga samun juna biyu.

Bayan da cikin ya bayyana, an ce tsohon ya matsa mata ta nemi zubar da shi ta hanyar amfani da magunguna da allurai, amma hakan bai yi nasara ba.

Lamarin ya fito fili ne bayan mahaifin yarinyar, tare da al’ummar anguwa, suka kai ta Hukumar Kare Hakkin Yara a ranar 5 ga Oktoba, 2025 domin sanar da abin da ke faruwa.

A lokacin, yarinyar na dauke da cikin watanni shida, inda jami’an hukumar suka karɓe ta tare da ba ta kulawa ta musamman a hannun kwararrun likitoci.

Daga bisani, ta haifi jariri namiji cikin koshin lafiya, kuma yanzu haka ita da jaririn na ci gaba da kasancewa a karkashin kulawar hukumar.

Darakta Janar na Hukumar, Barista Uma Mohammed, ya bayyana cewa ana ci gaba da kula da su yayin da ake shari’a kan lamarin.

Ya kara da cewa hukumar ce ke jagorantar shari’ar, yayin da ’yan sanda ke ci gaba da bincike domin gurfanar da wanda ake zargi, wanda a halin yanzu ke tsare.

Sakamakon binciken da aka gudanar ya hada da gwajin DNA, wanda ya tabbatar da cewa mutumin ne mahaifin jaririn.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *