
Tsohon Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar Janar Tukur Buratai mai ritaya, ya bayyana harin jirgin sama da aka kai kasuwar Jilli a matsayin matakin soja da ya zama dole domin kai hari kan sansanin ‘yan ta’adda.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, Buratai ya ce an kai harin ne bisa sahihan bayanan sirri da suka nuna cewa mayakan Boko Haram da ISWAP na amfani da kasuwar wajen gudanar da harkokin su da kuma jigilar kayayyaki.
Ya kuma amince da rahotannin da ke cewa an samu asarar rayukan fararen hula, inda ya bayyana hakan a matsayin abin takaici matuƙa.
Sai dai tsohon hafsan sojin ya yaba wa Rundunar Sojin Sama ta Najeriya da hukumomin tattara bayanan sirri bisa jajircewa da ƙwarewa da suka nuna wajen gudanar da wannan aiki.