Ɗan tsohon sarkin Iran ya buƙaci masu zanga-zanga su mamaye birnin Tehran.

Reza Pahlavi ya yi kiran ƙara fitowar masu zanga-zanga, yayin da yace yana shirin komawa ƙasar.
Katsewar intanet da aka yi a faɗin ƙasar ya taiƙata zanga-zangar.
Da safiyar yau ne dakarun sojin ƙasar suka sha alwashin kare muradun ƙasar da gine-gine da dukiyoyin gwamnati.
Wasu likitoci a wasu asibitocin ƙasar biyu sun shaida wa BBC cewa asibitocinsu sun cika da majinta – da suka ji rauni sakamakon zanga-zangar, ciki har da masu raunin harbin bindiga.
Iran ta zargi Amurka da kitsa zanga-zangar, zargin da Washintong ɗin ta musanta.
Shugaba Trump ya sha alwashin kai hari ƙasar idan aka kashe masu zanga-zanga.

