yan bindiga sun hana al’ummar Ƙaramar Hukumar Borgu a jihar Neja sakat
yan bindiga sun hana al'ummar Ƙaramar Hukumar Borgu a jihar Neja sakat

yan bindiga sun hana al’ummar Ƙaramar Hukumar Borgu a jihar Neja sakat

yan bindiga sun hana al’ummar Ƙaramar Hukumar Borgu a jihar Neja sakat

Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta tabbatar da cewa wasu ‘ƴan bindiga sun kai hari ƙauyen Damala da ke garin Woko a Karamar Hukumar Borgu ta jihar, inda suka kashe aƙalla mutum hudu.
Harin, wanda aka kai a makon da ya wuce, ya zo ne mako guda bayan da wasu ‘yan bindigar suka kashe mutane 42, ciki har da na kasuwar Daji da ke ƙauyen Demo, a ƙananan hukumomin Borgu da Agwara da ke makwabtaka da juna.
Mazauna yankunan karamar hukumar sun shaida wa BBC cewa suna zaune cikin fargaba da tashin hankali a kullum.
Mazauna yankunan sun ce saboda hare-haren da ‘yan binidgan ke kai wa a yanzu akwai wasu kasuwanni yankin da aka rufe.
Cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Neja, Wasiu Abiodun, ya fitar, ya ce maharan sun mamaye ƙauyen Damala ne da tsakar daren Asabar ɗin da ta gabata, inda suka kashe mutum huɗu tare da yin awon gaba da shanun da ba a tantance adadinsu ba.

 

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *