wuceHukumar ƙwallon ƙafa ta Afrika ta yi martani kan ƙorafin tawagar Senegal

Hukumar kwallon ƙafa ta Afrika (CAF) CAF ta yi watsi da iƙirarin da hukumar kwallon kafa ta Senegal (FSF) ta yi game da rashin adalci a tsare-tsaren da ake yi gabannin wasan ƙarshe na gasar cin kofin nahiyar Afirka (AFCON) da ke gudana a Morocco.

A wata sanarwa da ta fitar hukumar ta jaddada cewa ta yi ƙoƙarin tabbatar da daidaito tsakanin dukkan tawagogin da suka halarci gasar ta bana.

“Hukumar CAF ta himmatu kan tabbatar da adalci da gaskiya da kuma bin ƙa’idojinta ,” in ji sanarwar.

Ta kuma ƙara da cewa CAF ta yi aiki kafaɗa da kafaɗa da kwamitin tsare-tsaren gasar na cikin gida (LOC) don tabbatar da yanayi iri ɗaya ga dukkan tawagogin da ke halartar gasar.

Martanin na CAF dai na zuwa ne bayan Senegal ta fitar da wata sanarwa inda ta yi zargin rashin adalci a tsare-tsaren da suka shafi walwala da tsaron ƴanwasa gabannin wasan da za ta fafata da Morocco mai masaukin baƙi.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *