Jam’iyyar Issa Tchiroma ta ƙaurace wa zaɓen ƴan majalisa a Kamaru
Jam'iyyar Issa Tchiroma ta ƙaurace wa zaɓen ƴan majalisa a Kamaru

Jam’iyyar Issa Tchiroma ta ƙaurace wa zaɓen ƴan majalisa a Kamaru

Jam’iyyar Issa Tchiroma ta ƙaurace wa zaɓen ƴan majalisa a Kamaru

Jagoran adawar Kamaru, Issa Tchiroma Bakary, ya ce jam’iyarsa za ta ƙaurace wa zaɓen ƴan majalisa da na gundumomi na wannan shekarar, bayan da ya zargi gwamnatin ƙasar da ƙoƙarin “ƙwace ikon majalisa.”
A cikin wata sanarwa da kakakinsa ya fitar, Tchiroma Bakary – wanda ke zaman gudun hijira a Gambia – ya ce mambobin jam’iyyarsa ta CNSF ko kowace jam’iyya ta siyasa da ke shirin shiga zaɓen za su zama masu goyon baya ga rashin gaskiya kuma suna da hannu a ciki.
Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da wasu rahotonni ke cewa Bakary na duba yiwuwar komawarsa Kamaru, bayan ya tsere zuwa Gambiya bayan yayi iƙirarin lashe zaɓen shugaban ƙasar da ya gabata.
Tchiroma wanda ke kiran kansa da “shugaban Kamaru na gaskiya” ya jaddada cewa ba shi da niyyar sarayar da nasarar da ya samu a zaɓen da ya gabata
Duk da zarge-zargen maguɗi da rashin gaskiya a zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a shekarar da ya gabata, kotun tsarin mulki ta Kamaru ta bayyana Paul Biya, a matsayin wanda ya ci zaɓen shugaban ƙasa na 12 ga Oktoba.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *