Kwankwaso ya sake gindaya sharuɗa kan sauya sheƙa zuwa APC
Jagoran jam'iyyar NNPP yace Ba zan koma APC ba sai an faɗa min matsayina a jam'iyya - Kwankwaso

Kwankwaso ya sake gindaya sharuɗa kan sauya sheƙa zuwa APC

Kwankwaso ya sake gindaya sharuɗa kan sauya sheƙa zuwa APC

Jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya sake tabbatar da cewa ba zai koma jam’iyyar APC ba sai an cika masa wasu muhimman sharuɗa.
Jagoran ya bayyana haka ne yayin da ake ta raɗe-raɗin sauya sheƙarsa zuwa jami’yya mai mulki.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a gidansa da ke Miller Road a Kano, yayin da ya gana da magoya bayansa daga Ƙananan Hukumomin Rano da Dawakin Tofa.
Ya ce ba zai koma APC ba, sai an bayyana masa matsayinsa, makomar siyasarsa, da kuma makomar magoya bayansa da gwamnatin Jihar Kano.
“Dole ne a faɗa min matsayina, me ake nufi da wannan tafiya, da kuma yadda za a kare muradun talakawa, ciki har da matsayin magoya bayanmu da gwamnatin jihar Kano,” in ji Kwankwaso, kamar yadda mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Saifullahi Hassan, ya bayyana.
Wannan na zuwa ne a yayin da ake yaɗa jita-jitar cewa gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, zai sauya sheƙa zuwa APC, sai dai Kwankwaso ya sha nesanta kansa da sauya sheƙar.
Ya kuma soki masu asassa batun sauya sheƙar, inda ya ce kamata ya yi gwamnan da aka zaɓa a ƙarƙashin jam’iyyar NNPP ya ajiye amanar da aka ba shi kafin komawa wata jam’iyya.
Duk da haka, Kwankwaso ya nuna cewa bai rufe ƙofar sake yin tafiyar siyasa da wata jam’iyya ba, amma ya jaddada cewa hakan zai faru ne idan za a cika masa alƙawuran da yake so.
A farkon wannan makon, ya umarci magoya bayansa da ke aiki a gwamnatin jihar da su mara wa Gwamna Abba baya idan aka tilasta musu zaɓar wani tsagi.
A halin da ake ciki kuma, mataimakin gwamnan Jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ya fito fili ya nuna goyon bayansa ga Kwankwaso bayan dawowarsa daga ƙasar waje.
Ya halarcin taron da aka yi a ranar Laraba a gidan Kwankwaso, wanda hakan ya nuna kusancinsa da tafiyar Kwankwasiyya yayin da siyasar Kano ke ƙara ɗaukar zafi gabanin zaɓen 2027.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *