Gwamnatin Najeriya ta sha alwashin ƙarfafa dakarun ƙasar

Mataimakin Shugaban Ƙasar, Kashim Shettima ne ya bayyana haka a lokacin taron addu’o’i na musamman ga dakarun tsaron ƙasar da aka gudanar a Babban Masallacin Juma’a na ƙasa da ke Abuja, babban birnin ƙasar.
Shettima ya yaba wa gudunmowar da sojojin ƙasar da suka mutu a bakin aikinsu na kare kima da mutuncin ƙasar, da kuma kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
An gudanar da taron addu’o’in ne a wani ɓangare na bikin ranar tunawa gudunmowar da dakarun tsaron Najeriya ke bai wa ƙasar.
Gwamnatin ƙasar ce ta ware ranar 15 ga kowane watan Janairu domin karrama dakarun tsaron ƙasar.
Kalaman mataimakin shugaban ƙasar na zuwa ne a daidai lokacin da ake kara samun barazanar tsaro a ƙasar, inda a yan kwanakin nan ma shugaban Amurka ya yi barazanar sake kai hari Najeriya.

