
Gwamnan Jihar Borno Babagana Umara Zulum, ya amince da sauke dukkan mambobin Majalisar Zartarwa a Jihar nan take.
Wannan matakin na zuwa ne domin samar da yanayi mai kyau ga duk wani mamba da yake son tsayawa takara a zaɓe mai zuwa.
Gwamna Zulum ya umurci dukkan kwamishinoni da su miƙa al’amuran ma’aikatunsu ga Sakatarorin Dindindin kafin ranar Jumma’a, 3 ga Afrilu, 2026.
Wannan umurni zai tabbatar da cewa dukkan ayyuka da al’amuran gwamnati suna ci gaba da gudana ba tare da tangarda ba.
A cikin sanarwar da ofishin Gwamnan ya fitar, Zulum ya yi godiya ta musamman ga kwamishinonin da suka sauka bisa sadaukarwa da jajircewa, da gudummawar da suka bayar wajen ci gaban jihar da hidimar al’ummar Borno.
Ya bayyana cewa irin wannan himma ta taimaka matuƙa wajen ganin an samu cigaba a fannoni daban-daban na jihar.
Sanarwar ta kuma tabbatar da cewa matakin zai bai wa duk wanda ke da burin takara damar mai da hankali kan shirin neman muƙaminsa cikin sauƙi.