
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nada Abubakar Ibrahim Matawalle a matsayin Mai Riƙon Babban Daraktan Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar.
Sanarwar ta fito ne daga Daraktan Yada Labaran Gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, a ranar Litinin, 2 ga Fabrairu, 2026.
Abubakar Ibrahim Matawalle ya taba rike mukamin Babban Sakataren Hukumar Jin Daɗin Alhazai, sannan kuma ya yi aiki a matsayin babban sakatare a Ma’aikatar Kula da Ma’aikata kafin ritayarsa daga aikin gwamnati a shekarar 2014. Matawalle ya kuma jagoranci harkokin aikin hajji a lokuta daban-daban a jihar Kano.
Sanarwar ta ce wannan naɗi wani ɓangare ne na matakan gwamnatin jihar na cike guraben mukamai domin inganta gudanarwar muhimman hukumomi, kuma nadin ya fara aiki nan take.
Hakazalika, Gwamnan ya nada:
- Yusuf Mukhtar a matsayin Permanent Secretary.
- Barr. Rahama Malam Alhaji, a matsayin Provost, Kano State Anti-Corruption Institute.
- Jarumar Kannywood Aina’u Ade, daga Special Assistant zuwa Senior Special Assistant, Kannywood Affairs.
Sanarwar ta samu sanya hannun Babban Daraktan Yada Labaran Gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, a yau Litinin.

