
DA ƊUMI-ƊUMI: Majalisar Dattawa ta amince da dokar zaɓe bayan kammala nazari tare da amincewa da sashe 155.
Majalisar Dattawa ta amince da kudirin dokar zaɓe, inda ta yi gyare-gyare a wasu daga cikin sassan dokar, yayin da aka bar mafi yawan sassan kamar yadda suke tun farko.
Ɗaya daga cikin gyare-gyaren shi ne rage wa’adin da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ke da shi na wallafa sanarwar zaɓe daga kwanaki 360 zuwa kwanaki 180.
Sai dai kuma Majalisar ta ƙi amincewa da aikawa da sakamakon zaɓe ta hanyar lantarki(Electronic )kai tsaye (real-time) daga rumfunan zaɓe zuwa tashar tattara sakamakon zaɓe (IReV). Maimakon haka, ta zaɓi ci gaba da amfani da tanadin da ke cikin Sashe na 60 na Dokar Zaɓe ta 2022, wanda ke bai wa INEC damar aikawa da sakamakon zaɓe ta hanyar da ita kanta ta tsara.
Bugu da ƙari, a yayin duba kudirin sashe-sashe, Majalisar Dattawa ta tabbatar da Katin Zaɓe na Dindindin (PVC) a matsayin sahihiyar hanyar tantance masu kaɗa ƙuri’a, inda ta ƙi amincewa da amfani da hanyar lantarki(Electronic)ko wata madadin ta don tantancewa da aka gabatar a Sashe na 47.
