Ana muhara kan Ko APC da Tinubu za su iya hana tsige Fubara?

A ranar Alhamis, 8 ga watan Janairun 2026 ne dai majalisar jihar Rivers ta sake bijiro da batun yunƙurin tsige gwamna jihar, bayan musayar yawu da takun-saƙa da aka lura akwai a tsakaninsu.
Shugaban masu rinjaye na majalisar, Major Jack ne ya gabatar da takardar neman majalisar ta fara yunƙurin tsige gwamnan, bisa zarginsa da aikata manyan laifuka da ya ce sun saɓa da doka.
Ya ce sun yi la’akari ne da sashe na 188 na kundin tsarin mulkin Najeriya wajen tattarawa da tantace laifukan da suke ganin gwamnan ya yi, waɗanda kuma suke ganin sun saɓa da doka.

